A kokarinta na yaki da ta’addanci, Rundunar ‘yan Sandan Jihar Adamawa ta kama wasu mutum 3 daga cikin mambobin wata kungiya mai mutane biyar da ake zargin suna addabar mazauna babban birnin jihar, Yola, ta hanyar amfani da babura da Keke Napep.
A wata sanarwa da Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan (PPRO), SP Suleiman Nguroje, ya fitar a ranar Lahadi, ya bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne sakamakon sahihan bayanai da aka samu cewa kungiyar na kai hari da fashi ga mutanen da ke hanyarsu ta zuwa coci a kan titin Bishop da ke cikin yankin Jimeta-Yola.
Nguroje ya ce, da samun bayanin, jami’an ‘yan sanda sun yi saurin daukar mataki tare da isa wurin da lamarin ke faruwa, inda suka yi arba da wadanda ake zargin. An kama mambobi uku daga cikin yan kungiyar yayin da mutum biyu suka tsere.
“Da safiyar ranar 29 ga Disamba, 2024, jami’an ‘yan sandan Jihar Adamawa sun dauki mataki cikin gaggawa bayan samun rahoton cewa wasu matasa ‘yan Shila guda biyar suna kai hari da fashi ga mutane a hanyarsu ta zuwa addu’o’i na safe da sauran ayyuka a kan titin Bishop da ke cikin karamar hukumar Yola ta Arewa,” in ji Nguroje.
Rahotanni sun bayyana cewa, wadanda ake zargin sun kai wa jami’an ‘yan sanda hari da takubba da wukake yayin da suke kokarin kaucewa kame. A sakamakon haka, jami’an ‘yan sanda sun yi amfani da karfi don kwantar da tarzomar.
Kayayyakin da aka kwato sun hada da takubba, wukake, katunan ATM, wayoyin salula, da babur din Keke Napep, wadanda za ayi amfani dashi a matsayin shaida. Wadanda ake zargin da suka ji rauni suna karbar magani a wani asibiti na cikin gari kuma suna taimakawa wajen binciken yan sanda.
Nguroje ya tabbatar wa jama’a cewa karin bayani zai fito yayin da ake cigaba da bincike, sannan ya roki al’umma da su rika ba da rahoto kan duk wani abu mai kama da ayyukan ta’addanci ga hukumomin tsaro domin daukar matakin gaggawa.