Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya bayyana jimaminsa tare da isar da ta’aziyya ga Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu kan jerin mummunan mutuwa a turereniya da suka faru a Jihar Oyo, Babban Birnin Tarayya (FCT), da kuma Jihar Anambra, wanda ya jawo asarar rayuka da dama.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, tsohon Shugaban ya mika ta’aziyya ga Gwamna Seyi Makinde na Jihar Oyo, Farfesa Chukwuma Soludo na Jihar Anambra, da kuma Nyesom Wike, Ministan FCT.
Ya roki shugabannin su isar da sakon ta’aziyyarsa da goyon bayansa ga iyalai da sauran yan uwan wadanda suka rasa rayukansu, tare da fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata a tarzomar turereniyar.
Haka kuma, tsohon Shugaban Kasa ya mika ta’aziyyarsa ga al’ummar Katolika da abin ya shafa a Abuja.