Hedikwatar tsaron Najeriya ta bayyana jagoran ’yan bindiga, Bello Turji, a matsayin gawa.
Hedikwatar ta yi wannan bayani ne bayan barazanar da Turji ya yi wa sojoji da al’ummomi a jihar Zamfara.
Da yake mayar da martani yayin taron ƙarshen shekara da aka gudanar a Abuja, Daraktan hulɗa da jama’a na hedikwatar tsaro, Manjo Janar Edward Buba, ya yi watsi da barazanar Turji, yana mai bayyana ta a matsayin maganar banza.
Ya kuma sha alwashin cewa “kwanakin Bello Turji a duniya sun fara ƙidaya.”
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da farfagandar da jagoran ’yan ta’addan ke yaɗawa game da abin da ya faru a Sakkwato, yana mai cewa ’yan ta’adda na amfani da farfaganda ne domin karkatar da hankalin mutane.