Mazauna Yargaladima da ke jihar Zamfara sun musanta bayanin da rundunar ‘yan sanda ta bayar kan fashewar bama-baman da ya faru a kan titin Gusau-Dansadau, inda suka ce harin ba shi da nasaba da Lakurawa.

A cewarsu, ‘yan bindiga ne su ka dasa bama-baman da suka tashi a wurare biyu.

Wani mazaunin yankin, Malam Ibrahim Usman, ya danganta harin da wani shahararren shugaban ‘yan bindiga mai suna Dogo Gide.

Da yake magana da manema labarai a Gusau, Usman ya zargi rundunar ‘yan sanda da yin rufa-rufa, yana mai cewa ba sa son bayyanawa duniya gaskiyar lamarin.

Ya ce Gide da mutanensa sun yi niyyar kai hari kan unguwar Yargaladima ne don daukar fansa bayan kashe wani shugaban ‘yan bindiga mai suna Sani Black da mutanen kauyen suka yi kwanan nan.

“Wannan harin ba shi da alaka da ‘yan ta’addan Lakurawa.

“An tsara shi ne daga mutanen Dogo Gide. Sun dade suna shirin kai hari kan al’ummar nan amma ba su yi nasara ba saboda mun kasance cikin shiri.

“Amma a wannan karon, sun dasa bama-baman a kan hanya bayan sun samu labarin cewa jami’an tsaro na kan hanyarsu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa ‘yan ta’addan Lakurawa, wadanda ya ce sun fito ne daga kasashen Nijar da Mali, sun sha bamban da Fulani ‘yan bindiga da ke aiki a jihar Zamfara.

“Wadannan ‘yan bindiga na cikin kungiyar Buharin Daji da ya rasu, kuma yanzu Dogo Gide ke jagoranta. Su mutanen gari ne, ba kamar Lakurawa da ‘yan sanda suka ambata ba,” in ji shi.





Source link