Al’umma sun fara martani kan batun amincewar gwamnoni wajen kafa yan sandan Jihohi, a Alhamis din nan ne dai gwamnan Kaduna Malm Uba Sani yace gwamnoni sun amince da batun kirkirar yan sandan jihohi a wani taro da suka gabatar a Larabar da ta gabata.

Daya daga cikin wadanda suka ga baiken wannan mataki shine dattijon Kasa daga Kano, Alhaji Ali Babba Dan’agundi, wanda a tattaunawarsa da Daily Post Hausa ya gargadi yan majalisu da kada su amince da wannan shawara, da acewarsa zata kaa gurgunta lamura ne kawai.

Ya ce “Gwamnnoni su ne matsalar kasar nan, kowa yana ganin irin abinda suke yi, duk lalacewar gwamnatin tarayya tafi gwamnonin adalci”

Alhaji Ali Babba Dan Agundi ya kuma yi kira ga yan majalisu da suran jama’a da akad su yarda da wannan mataki, “Kada dan majalisar da ya yarda da wannan domin kuwa zai kara maida mu baya, idan gwamnoni na son taimakawa sai su kara yawan yan sanda a fadin kasa baki daya, ga matasanmu nan ba aiki, suna ta kokarin shiga ayyukan tsaron.”

 





Source link